GWAMNATIN KANO TA SHIGAR DA FURSUNONI CIKIN TSARIN INSHORAR LAFIYA KYAUTA
A wani mataki na musamman don inganta walwalar al’umma, Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shigar da dukkan fursunonin jihar cikin tsarin inshorar lafiyarta, domin samar musu da ingantaccen kula da lafiya kyauta yayin da suke tsare.
Wannan sanarwa ta fito daga bakin Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, shugabar Hukumar Taimakon Lafiya ta Jihar Kano (KACHMA), yayin wata ziyara da ta kai ofishin shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na jihar, Ado Salisu, a yau Litinin.
Dr. Rahila ta bayyana cewa wannan shiri ya samu amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya ke da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowa, har da fursunoni, ya samu damar cin gajiyar romon dimokuradiyya. Ta ce tsarin inshorar lafiyar zai ba fursunoni damar samun cikakkiyar kulawar lafiya kyauta a duk lokacin da suke tsare.
Shugabar ta tabbatar wa hukumar kula da gidajen gyaran hali cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa fursunoni ta fuskar lafiyar jiki da sauran bukatun su.
A cewar ta, “Muna kira ga fursunonin da su ci gaba da yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’a, domin wannan matakin ya nuna tsantsar kishin al’umma da gwamnatinsa ke da shi.”
Wannan mataki ya janyo yabo daga masu lura da al’amuran yau da kullum, inda ake kallonsa a matsayin wani bangare na tsare-tsaren gwamnatin Kano wajen tabbatar da walwalar kowane dan kasa, ba tare da nuna bambanci ba

0 Comments