Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , ya jagoranci gagarumin shirin rabon kayan makaranta kyauta ga daliban jihar.
A wannan muhimmin taro, Gwamnan ya mika kayan makarantar ga Shugabannin Kananan Hukumomi da Sakatarorin Ilimi na Kananan Hukumomi.
Wannan tallafi na kayan makaranta yana cikin kudirin gwamnatin Kano na inganta ilimi da saukaka nauyin da iyaye ke dauka wajen ciyar da 'ya'yansu ilimi.
Gwamnatin ta himmatu wajen tabbatar da cewa kowane yaro a Jihar Kano yana da kayan da za su taimaka masa wajen samun nasara a karatunsa.
Wannan mataki na Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna jajircewarsa kan inganta ilimi a Kano tare da kara wa iyaye kwarin gwiwa don ci gaba da tura 'ya'yansu makaranta.

0 Comments