Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, CON, PhD, zai farfaÉ—o da gidan Marigayi Jarman Kano Alhaji Muhammad Adamu Dankabo, Mai Kamfanin Jirgin sama na Kabo Air.
A wata sanarwa da sakataren Masarautar Kano Danmakwayon Kano Alhaji Abba Yusuf ya fitar, Sarkin Kano Khalifa Sanusi II zai nada Babban Dan Marigayin Alhaji Idris Muhammad Adamu Dankabo a matsayin Sarkin Gabas din Kano Hakimin Kabo. Nadin Wanda za’ayi ranar jumu’a 27 ga watan disambar da mukeciki na shekarar 2024 za’ayi shi ne a fadar Masarautar Kano dake gidan Rumfa da karfe 9 na safe.
Wannan yana cikin Æ™udurin Mai Martaba Sarki na farfaÉ—o da gidaje muhimman mutane a Kano da aka manta da su, dan cigaba da karfafar zumunci da adalci tsakanin Al’ummah.
Kuci gaba da bibiyarmu domin samun wasu sabbin labarai

0 Comments