YANZU-YANZU: GWAMNA ABBA KABIR YUSUF YA SA HANNU A KASAFIN KUÆŠIN 2025
A wani muhimmin mataki na ci gaba da inganta rayuwar al’ummar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuÉ—in shekarar 2025.
Wannan kasafin kuÉ—i ya kunshi manyan tsare-tsare na ayyukan raya kasa da suka shafi bunkasa ilimi, kiwon lafiya, gine-ginen hanyoyi, da samar da aikin yi ga matasa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta tabbatar da adalci wajen aiwatar da dukkan shirye-shiryen da aka sanya a cikin kasafin kuÉ—in.
Sanya hannu kan kasafin kuÉ—in ya nuna jajircewar gwamnatin Kano wajen ci gaba da cika alkawuran da ta dauka ga jama’a, tare da tabbatar da cewa kowa ya samu romon dimokiradiyya.

0 Comments