GWAMNATIN JIHAR KANO TA BUDE KOFAR DAMA GA MASU DIGIRI 2:1!
Biyo bayan umarnin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , na sanya masu digirin 2:1 cikin jerin wadanda za su iya neman tallafin karatun digiri na biyu a jami’o’in cikin gida, mutane da dama sun yi dafifi don gabatar da takardunsu.
Wannan dama ce ta musamman da Gwamnatin Jihar Kano ke bayarwa domin tallafawa matasa masu sha’awar cigaban ilimi tare da bunkasa hazakar ‘yan asalin jihar.
Jama a naganin wannan mataki ya kara nuna irin jajircewar gwamnatin jihar wajen ciyar da ilimi gaba tare da ba wa kowa dama.

0 Comments