SOJOJIN NIGER NA NEMAN DAUKIN KASAR RASHA

Gwamnatin mulkin sojin Nijar na neman É—auki daga Rasha
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane


Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani
Dakarun sojin Nijar da suka yi wa gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum juyin mulki na kira ga ƙasar Rasha da ta kawo musu dauki, tare da neman ƙasar Faransa da sauran ƙasashen yamma da ke ƙasar da su fice da Nijar ɗin.


Cikin wata sanarwa ta kakakin majalisar ceto ƙasar ta sojoji Kanal Manjo Amadu Abdurahamane, ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya yi kira ga ƙasar Rasha da ta taimaka wa Nijar da sojoji da kayan aiki.


A yau ne ƙungiyar Ecowas ke gudanar da taro don tattauna batun juyin mulkin da sojojin suka yi a Nijar.


To sai dai cikin sanarwar da majalisar ceton ta Nijar ta fitar, ta yi zargin cewa taron na Ecowas yunƙuri ne far wa Nijar da yaƙi.

A don haka ne ma Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya ce a shirye suke su kare ƙasarsu daga hare-haren da ya yi zargin Ecowas za ta ƙaddamar wa ƙasar.

Sannan kuma ya yi kira ga 'yan ƙasar da su fito su gudanar da zanga-zanga domin mara musu baya.
Kakakin majaliar ceton Nijar Kanal Manjo Amadu AbdurahamaneImage


 Kakakin majaliar ceton Nijar Kanal Manjo Amadu Abdurahamane

Ƙasar Rasha dai na da dakaru a Mali mai makwabtaka ta Nijar, lamarin da ya sa Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka janye sojojinsu da ke aikin wanzar da zaman lafiya daga ƙasar.


A ranar Laraba ne dai sojojin Nijar suka sanar da kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, lamarin da ya sa ƙasashen duniya da ƙungiyoyi ke ci gaba da yin Allah wadai da abin da sojojin suka yi, tare da kira da su maido da mulkin fara hula da kuma sakin shugaban ƙasar wanda suke tare da shi.


Ko a ranar Asabar ma Æ™ungiyar haÉ—in kan Afirka ta AU ta bai wa sojojin Æ™asar wa'adin kwanaki 15 da su koma barikokinsu tare da maido da mulkin fara hula a Æ™asar. 

Post a Comment

0 Comments