BANKIN NIGERIA ZAISHA BINCIKE - TINUBU

Shugaba Tinubu ya naÉ—a mai bincike na musamman kan Babban Bankin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naÉ—a wani mai bincike na musamman mai suna Jim Osayande da zai yi bincike a babban bankin Najeriya.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Tinubu ya aika wa Obazee, shugaban hukumar masu bayar da rahotannin harkar kuÉ—aÉ—e ta Najeriya.


Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da alaƙa da bankin ta hanyar amfani da ƙwararru da hukumomin tsaro da masu yaƙi da rashawa da suka dace don aiwatar da aikin.


Tinubu ya kuma aikewa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin.


Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Emefiele ke fuskantar shari'a kan zargin taimaka wa ta'addanci, sai dai ya musanta zargin.


Kotu dai tabada belin tsohon dakataccen governornon bankin 


Post a Comment

0 Comments