Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da ƙudirin Sanatocin yankin kudu maso gabas na neman a saki Nnamdi Kanu shugaban ƙungiyar ƴan a ware ta Biafra (IPOB).
Sanatan Imo ta Yamma, Osita Izunaso, wanda ya gabatar da Æ™udirin, ya ce sakin Kanu zai kawo Ƙarshen umarnin zama a gida da ‘yan bindiga ke aiwatarwa a yankin.
"Lokacin da aka tilasta wa mutane zama a gida da kuma rufe kasuwanci, raguwar kayan aiki da raguwar samun kuÉ—in shiga, yana shafar rayuwa da ci gaban tattalin arziki," in ji shi.
Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da roƙon da ɗan majalisar ya yi, inda a maimakon haka ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da kama waɗanda suka aiwatar da wannan umarni.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suna aiwatar da umarnin zama a gida duk ranar Litinin tun watan Agustan 2021 duk da cewa IPOB ta nisanta kanta da su.
Tun a watan Yunin 2021 ake tsare da Mista Kanu bayan da kotu ta yi watsi da tuhumar da ake masa kan ta'addanci a watan Oktoban 2022.
Hakan na nufin neman asaki Nnamdi kanu yagamu da cikas a majalisar inda take ganin gwara akama masu bada umarnin
Domin ayi musu hukunci da doka ta tanazar

0 Comments