Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya gargaɗi sabbin kwamishinoni 14 da ya rantsar kan buƙatar gujewa rayuwar bushasha.
Gwamnan ya kuma ƙaddamar da gidauniyar tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al'umma.
Da yake rantsar da sabbin kwamishinonin, gwamnan ya ce yanzu gwamnatinsa ta haɗa abokan aikinta kuma ta yi aniyar kawo sassauci ga jama'ar jihar, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Uba Sani yanzu lokaci ne na ƙara ɗaura ɗamara kuma “Dole mu ɗauki matakan rage kashe kuɗi wajen tafiyar da gwamnati , dole ne mu ƴan siyasa mu nuna wa jama'ar mu irin rayuwar da ya kamata kowa ya yi ta sadaukarwa don ci gaban ƙasa”
Yana kiranne adai dai lokacin da yan nigeria ke fuskantar tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin fetur da gwamnatin tinubu tayi
Abinda ya haifarda tsadar kayayyaki

0 Comments