GWAMNATIN KANO TA TARBI DALIBAN DA SUKA KAMMALA DIGIRI NA BIYU A INDIA
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar Gwamnatinsa wajen tarbar daliban asalin Jihar Kano da aka tura kasar India domin karo karatun Digiri na Biyu. Daliban sun samu nasarar kammala karatunsu, kuma yau sun dawo gida cikin alfahari.
A yayin wannan taro, Mai Girma Gwamnan ya nuna farin cikin sa da wannan gagarumar nasara, tare da jaddada kudirin Gwamnati na cigaba da zuba jari a harkar ilimi domin inganta rayuwar matasa da bunkasa cigaban Jihar Kano.
A tare da Gwamnan akwai Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda kuma shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, H.E Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, da wasu manyan jami’an Gwamnati.
Wannan nasarar naga cikin kokarin sauke alkawarinda Gwamnatin Kano yayi wajen cika alkawurran ta na bai wa ilimi muhimmanci, tare da tabbatar da cewa daliban jihar na samun damar da ta dace domin su kasance manyan gobe.

0 Comments