Gamayyar wasu Æ™ungiyoyi sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin daÉ—i kan abin da suka kira matsi da Æ™uncin rayuwar da ‘yan kasar suka tsinci kansu a ciki.
‘Yan Æ™ungiyoyin waÉ—anda suka bazu kan wasu titunan Kano, sun haÉ—ar da Æ™ungiyar dalibai, inda suke neman gwamnati ta sassauta yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa.
Masu zanga-zangar maza da mata, wasunsu É—auke da allunan rubuce-rubuce, sun yi korafi a kan wahalhalun da suka ce janye tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, ya jefa mutane cikin mawuyacin hali.
Ƙungiyoyin sun hada da na mata da ɗalibai da kuma masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam.
ÆŠaya daga cikin masu zanga-zangar, Kwamared Fatima Muhammad Umar ta ce babban abin da ya fi tayar mata da hankali shi ne mata ne suka fi shiga tasku sanadin wahalhalun da ake fama da su a Najeriya.
Itama dai ƙungiyar kwadago sun shirya gudanar datasu gobe laraba
Dukda rundunar yan sanda ta ƙasa ta gargaɗesu dan kar abin yazama matsalar tsaro aƙasa

0 Comments