MATAIMAKIN JAM'IYYAR APC YA SAUKA


SHUGABANCIN APC
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai wakiltar shiyyar arewa maso yamma, Malam Salihu Lukman ya ajiye muƘaminsa.

A yau Laraba ne ya miƙa takardar ajiye aikinsa ga muƙaddashin shugaban jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Abubakar Kyari.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan tsohon shugaban jam'iyyar, Sanata Abdullahi Adamu da kuma sakatarenta na Ƙasa Sanata Iyiola Omisore suka yi murabus.

A cikin sanarwar, Malam Salihu Lukman ya ce ya ajiye muƙamin nasa ne saboda zargin shisshigi wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar, wanda ya saɓa turbar da aka kafa jam'iyyar a kai.

Ya ce ya zaɓi yin murabus ne saboda baya son ci gaba da zama a wajen da ake yi wa fafutukar neman kawo gyaran da yake yi a matsayin yunkurin turjiya.


Wasu rahotanni dai na nunida cewa tsohon gwamnan jihar Kano
Alhaji Abdullahi umar ganduje zai iya zama shugaban jam'iyyar ta APC na Æ™asa 

Sakamakon goyon bayan da yake samu 


Post a Comment

0 Comments