Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi da cewa su dakata.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sabon zaɓaɓɓen gwamnan Sunusi Bature Dawaki Tofa ya fitar, sabon gwamnan ya shawarci masu bai wa gwamnatin jihar bashi na cikin gida da na waje da kada su amince da bai wa gwamnatin jihar bashi daga ranar 18 ga watan Maris zuwa ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sabuwar gwamnatin ba za ta yi la'akari da bashin da jihar ta karɓa, ba tare da saninta ba daga ranar zaɓe zuwa ranar da aka rantsar dasabuwar gwamnatin.
Haka kuma sanarwar ta ce masu bin gwamnatin jihar bashi a yanzu su kwana da sanin cewa za a sake nazarin ƙa'idojin bashin bayan kammala bincike a kan kowanne bashi da ake bin jihar.
Ko a makon da ya gabata ma sabon zaɓaɓɓen gwamnan ya bayar da shawara ga masu gine-gine a filayen gwamantin jihar da su dakatar da ayyukansu.
To sai dai 'yan kwanaki bayan shawarar zaɓaɓɓen gwamnan, gwamnan jihar mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya mayar masa da martani, yana mai cewa sabon gwamnan ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama'a.
A sanarwar da kwamshinan yaɗa labaran jihar Muhammad Garba ya fitar ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, a daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu yake kan mulki, tamkar riga mallam masallaci ne.

1 Comments